El Clasico: Ko yaya zata kaya a ziyarar da Barca za ta kai wa Madrid

0
52

Real Madrid zata karbi bakuncin Barcelona a wasan Clasico na ranar Lahadi a Santiago Bernabeu, inda ta kasance a saman teburin gasar La Liga.

Kulob din ya fitar da Yuro miliyan 145 a bazara wajen siyan ‘yan wasa, duk da matsalolin kudi da kungiyar ke ciki, sai dai alkaluman na nuna cewa kungiyar na samun riba ta hanyar masu kallon wasa a filin ta.

A kakar bana dai tuni Barcelona ta ci kwallaye bakwai a wasanni hudu da ta buga a gasar zakarun Turai, inda ta yi rashin nasara a wasanni biyu, ta yi kunnen doki daya, ta kuma yi nasara a kan daya.

Wasan da suka tashi 3-3 da Inter Milan a ranar Laraba, hakan na nufin kocin Barcelona Xavi na cikin wani yanayi na rashin tabbas, ganin yadda ake hasashen cewar kungiyar na iya komawa gasar Europa.

Inter dai kawai tana bukatar doke Viktoria Plzen wadda kawo yanzu aka zura mata kwallaye 16 a wasanni hudu domin tabbatar da cewa Barcelona ba ta tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai ba, wanda hakan idan ya tabbata kaga kenan karo na biyu a jere za buga wasa a Europa.

Barcelona da Real Madrid na kan-kan-kan ne a saman teburi Laliga a kakar gasar ta bana, kuma babu wacce tayi rashin nasara tun bayan fara gasar a bana, sannan kuma maki biyu-biyu ne suka baras.

RFI