Ali Nuhu ya maka jaruma Hannatu Bashir a kotu

0
61

Jarumin Kannywood Ali Nuhu ya kai ƙarar babbar furodusa Hannatu Bashir a kotu bisa zargin ta ci masa mutunci ta hanyar gaya masa magana a saƙon tes.

Lauyar Ali, wato Salima Muhammad Sabo ta ofishin lauyoyi na M.L. Ibrahim & Co., ta shigar da ƙarar ne a Kotun Majistare mai lamba 58 da ke unguwar Nomansland a Kano.

Majiyar Focus News Hausa, Mujallar Fim ta gano cewa Ali Nuhu ya yi ƙarar ne saboda akasin da aka samu kan aikin wani fim na Hannatu wanda aka yi alƙawari da shi zai yi, amma ya saɓa.

A ranar da aka yi alƙawari da shi zai je ɗaukar fim ɗin, wato 10 ga wannan watan na Oktoba, an tafi aikin ɗaukar fim ɗin, amma sai Alin bai samu zuwa lokeshin ɗin ba domin ya yi tafiya, ba ya gari.

Rashin zuwan nasa ya sa tilas aka ɗage ɗaukar ɓangaren sa a aikin zuwa rana ta gaba, amma a wannan ranar ma bai je ba. Kamar yadda ya faɗa masu, ya ce sai a ranar ne ma zai dawo kuma ko ya dawo ma ba zai samu zuwa ba sai dai a rana ta gaba.

Wannan abin ya ɓata ran Hannatu Bashir, wadda ita ma sananniyar jaruma ce, don haka ta tura masa saƙo a waya ta ce masa ba ta ma buƙatar aikin da shi.

Saƙon, wanda mujallar Fim ta gani, ya sa shi ma jarumin ya mayar mata da martani mai zafi, ya ce ta yi masa rashin kunya. Daga ƙarshe ya faɗa mata zai ɗauki mataki na shari’a a kan ta. Ita kuma ta ce to ta na jiran shi.

A takardar ƙarar mai shafi biyu, wadda lauyar sa ta shigar, Ali ya shaida wa kotun cewa Hannatu, mai kamfanin Hanan Synergy Concept Limited, ta tura masa tes ne a ranar 10 ga Oktoba inda ta faɗa masa cewa ya ƙi zuwa yi mata aikin fim kuma hakan da ya yi mata bai dace ba kuma zalunci ne.