HomeLabaraiReal Madrid ta doke Barcelona da ci 3-1

Real Madrid ta doke Barcelona da ci 3-1

Date:

Related stories

Hukumar DSS ta kama wasu bata gari da ke sayar da sabbin takardun kudi na Naira

Ma’aikatar harkokin wajen kasar a ranar Litinin din nan...

Yadda lamari ya kasance yayin zuwan Buhari Kano don kaddamar da aiyuka 8

An tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Kano da...

Najeriya ta yi asarar likitoci 2800 a cikin shekaru biyu – NARD

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya NARD, Dr Innocent Orji ya...

Yadda ake canzar da kudin Sepa zuwa Naira a yau Litinin

Farashin Separ Nijar zuwa Naira a farashin kasuwar canjin...

Real Madrid ta yi galaba a kan babbar abokiyar hamayyarta Barcelona wadda ta lallasa da ci 3-1 a filin wasa na Bernabeu a ranar Lahadin nan.

Wasan wanda shi ne na tara a Gasar La Liga, ya bai wa Real Madrid damar yin zaman dabaro a saman teburin gasar da tazarar maki uku tsakaninta da Barcelona.

Madrid wadda ke kare kambun gasar La Ligar, ta yi wa Barcelona shigar wuri yayin da ta jefa mata kwallaye biyu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ta hannun Karim Benzema da Federico Valverde.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne Barcelona ta huce takaici inda ta zare kwallo daya ta hannun Ferran Torres saura minti bakwai a tashi wasan.

Sai dai kungiyar wadda Carlo Ancelotti ke jagoranta, ta jaddada nasararta da tabbatar da samun maki uku a wasan yayin da ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma Rodrygo na kasar Brazil ya sa kwallon a koma.

A halin yanzu dai babu wata kungiya da ta yi galaba a kan Madrid tun da aka soma La Ligar bana, inda tuni ta hada maki 25 yayin da Barcelona da ke biye mata ta hada maki 22.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories