Tinubu ya ziyarci Sarkin Zazzau bayan tafiyar Atiku

0
53

Dan takarar shugabancin Najeriya a Jam’iyyar APC, Bola Tunubu, ya ziyarci Fadar Sarkin Zazzau jim kadan bayan tafiyar dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a ranar Asabar.

Tinubu wanda ya je Jihar Kaduna don halartar Taron Koli kan Zuba Jari da Bunkasa Masana’antu, ya ce ziyarar tasa ta karramawa ce da neman albarkar sarki.

A cewarsa zai sake dowawa fadar nan ba da jimawa ba don kaddamar da yakin neman zabe don karbar ragamar shugabancin Najeriya a shekarar 2023.

Tun farko, da yake nashi jawabin, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya marabci Bola Tunubu ne saboda ziyarar da ya zo, kuma ya ce suna yi masa fatan alheri tare da goyon baya a zabe mai zuwa.

Da yake maida jawabi, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya gode wa ayarin Tinubu saboda ziyarar da suka kawo masa.

Ya kuma ya yi kira ga dan takarar ya yi amfani da yakin neman zabensa wurin hadin kai da kawo cigaba mai dorewa tsakanin al’ummar Najeriya.