Ambaliyar Ruwa: Mutum 603 sun mutu, miliyan 1.3 sun kaurace wa muhallinsu

0
38

Gwamnatin tarayya ta ce akalla mutane 603 ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa a fadin Nijeriya tare da raba mutane miliyan 1.3 daga muhallansu.

Jihohin da aka samu rahoton mutuwar mutanen sakamakon ambaliyar ruwan sun hada da Kogi, Anambara, Kebbi, Delta, Bayelsa, da kuma Jigawa sai jihohi kusan 31 da aka samu rahoton ambaliyar ruwan ta shafe su a shekarar 2022.

Ministar kula da agajin jin kai da bala’o’i da ci gaban jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa kimanin gidaje 82,053 sun lalace gaba daya, mutane miliyan 2,504,095 ne abin ya shafa, yayin da hekta 332, 327 na fili ta lalace gaba daya.

Da take bayyana alkaluman a jiya a Abuja, yayin wani taron manema labarai, ministar ta ce, gaskiya ne ‘yan Nijeriya na iya razana kan yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a fadin kasar nan, amma bai kamata su firgita ba kan barazanar rashin samun wadataccen hatsi a shekarar nan.

Wasu alkaluma sun nuna cewa adadin wadanda suka samu raunuka sanadiyyar ambaliyar ya kai 2,407, yayin da gidajen da suka lalace ya kai 121,318, sai gonakai da suka lalace 108,392.

Sadiya Umar Farouq ta ce an gargadi gwamnatocin jihohin sau da yawa, amma sun kasa daukar matakan da suka dace don rage yawan asarar da ambaliyar ruwan ke yi.