An kori shugaban hukumar tsaron intanet na Jamus saboda zargin alaka da Rasha

0
47

An kori shugaban hukumar hana kutse a shafukan intanet na kasar Jamus saboda zargin alaka ta kut-da-kut da kasar Rasha ta hanyar wata kungiya da ya taimaka wajen kafuwarta.

Arne Schönbohm shi ke jagorantar hukumar tsaron intanet din kasar (BSI) – wadda ke da alhakin tsaron shafukan sadarwar gwamnati – tun shekarar 2016.

Kafofin yada labaran kasar sun zarge shi da alaka da mutanen da ke aiki a hukumar tattara bayanan sirri na kasar Rasha.

Ma’aikatar cikin gida ta kasar ta ce an kaddamar da bincike game da zarge-zargen da ake yi masa, ta kuma tabbatar da korarsa daga aiki nan take.

Kafin nada shi a matsayin shugaban hukumar BSI, mista Schönbohm ya taimaka wajen kafa wata cibiyar tsaron shafukan intanet a kasar, wata kungiyar mai zaman kanta da ke bayar da shawarwari ga hukumomi kan abubuwan da suka shafi tsaron intanet.

An kuma ce har yanzu yana da kyakkyawar alaka da kungiyar, inda har ma a watan Satumba ya halarcin bikin cikarta shekara 10 da kafuwa.