Kamfanin BUA ya ce baya bukatar filin da jihar Kogi ta mallaka masa

0
28

Kamfanin BUA dake Najeriya ya bayyyana cewar baya bukatar fili kadada dubu 50 da ya saya a Jihar Kogi a shekarar 2012 domin gina masana’anta saboda rashin ingancinsa.

Wata wasika da Kamfanin ya rubutawa gwamnatin Jihar Kogi wadda tayi barazanar kwace filin, tace kamfanin ya bayyana dalilan da suka sanya shi kasa gudanar da aiki a filin tare da kin biyan kudin mallakarsa.

Kamfanin BUA yace matsalar tsaro da rashin hanya da kuma rashin kayan more rayuwa na daga cikin dalilan da suka sanya shi sake tunani akan mallakar filin da ake takaddama akai.

Wasikar tace tun bayan da Kamfanin ya amsa gayyatar zuba jari a Jihar Kogi a shekarar 2012, babu wani yunkuri da gwamnatin jihar tayi wajen samar da hanya ko kayan more rayuwar da zai karfafa masa amfani da filin kamar yadda suke bukata.

BUA yace yanzu haka babu hanyar zuwa filin da ake magana akai sai ta cikin ruwa, kuma matsalar tsaro a wurin ta sa ba zasu iya zuba jarinsa a filin ba kamar yadda suke bukata.

Kamfanin yace binciken masana da suka yi a filin ya nuna musu cewar kashi 30 ne kawai na filin ke da inganci, yayin da kashi 66 duk duwatsu ne da tsaunuka wadanda ba zasu basu damar gudanar da aikin da suke bukata ba.

Saboda wadannan dalilai Kamfanin BUA ya shaidawa gwamnatin jihar Kogi cewar baya bukatar filin kuma sun dakatar da shirin zuba jarin da suke da shi a wurin.

Kamfanin yace da filin ya cika muradunsu da tuni sun biya shi kafin fara duk wani aiki kamar yadda manufofinsa yake a ko ina, saboda haka gwamnatin jihar Kogi na da hurumin soke takardar mallakar filin ba tare da wani haufi ba.

Wannan takaddama na BUA da gwamnatin Jihar Kogi na zuwa ne kasa da mako guda bayan wadda aka fara tsakanin gwamnatin jihar da Kamfanin simintin Dangote wanda ya kaiga rufe kamfanin dake Obajana.

Kungiyar Yan kasuwa da masu zuba jari a Najeriya tare da masana tattalin arziki na bayyana damuwa akan wannan dambarwa wadda ke barazana ga ayyukan jama’a da kuma shirin zuba jari a Najeriya.