Najeriya ta yi martani kan harin da aka kai wa ‘yan ƙasarta a Jami’ar Indiya

0
47

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu rubutaccen tabbaci daga Hukumomin Indiya cewa za su kare ɗalibanta da ke can.

Shugabar Hukumar kula da harkokin ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙetare, Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana haka lokacin da take mai da martani ga rahotannin cewa an kai wa ‘yan Najeriya hari a wata jami’ar ƙasar Indiya.

A ranar Litinin ne, wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda rigima ta kaure a wata harabar jami’ar da ke birnin Delhi.

Wani Farfesa a fannin binciken rikice-rikice da zaman lafiya, Ashok Swain ne yaɗa bidiyon rigimar a dandalin tiwita inda ya rubuta cewa;”Ana far wa ɗaliban Najeriya da suka zo karatu ƙasar Indiya a harabar wata Jami’a da ke kusa da birnin Delhi – ɗaliban Najeriya 30,000 ne suka biya kuɗi don yin karatu a Indiya, yayin da ‘yan Indiya 50,000 ke zaune a Najeriya suna neman kuɗi. “