Zanyi duk mai yuwa wajen magance tsadar kayan abinci – Buhari

0
100

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta dukufa kan kokarin magance tsadar farashin abinci a kasar.

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake bude taron bita kan ayyukan ministocinsa karo na uku don tantance irin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da kudurorin da gwamnatinsa ke bai wa fifiko.

Aminiya ta ambato Buharin yana cewa: “Muna yin gagarumin kokari don warware matsalar tashin farashin abinci mai alaka da hauhawar farashin da ake fama da shi a fadin duniya.”

Alkaluman baya-bayan nan, in ji shi daga Hukumar Kididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar farashin kasar ta kai kashi 20.77 a watan Satumba.

Hukumar ta ce hauhawar farashin abiinci ta karu ne sakamakon karuwar farashin burodi da hatsi da sauran kayan abinci irinsu dankalin turawa da doya da man girki.

A yayin taron, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan raya kasa masu gagarumin tasiri a faɗin kasar, don haka shugabancinsa ya cimma muradai da burukan ‘yan Najeriya.

Ya nanata irin ci gaban da aka samu a fannoni kamar aikin gona da tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa da tsaro da kula da lafiya da yaki da cin hanci da rashawa.