HomeLabaraiAmbaliyar ruwa ya lalata asibitoci da makarantu 257 a Jigawa - UNICEF

Ambaliyar ruwa ya lalata asibitoci da makarantu 257 a Jigawa – UNICEF

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Majalisar Dinkin Duniya tace ambaliyar ruwan da aka samu a Najeriya daga watan Agustan bana ta lalata makarantu da asibitoci 257 a jihar Jigawa, yayin da tayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Babban jami’in kula da ilimi na Hukumar UNICEF Michael Banda ya gabatar da wadannan alkaluma lokacin da ya jagorani tawagar da ta kai kayan agajin da kudinsu ya kai naira miliyan 231 ga mutanen da iftila’in ya shafa a Jihas.

Banda yace mutane da dama sun rasa gidajen su da gonakinsu da kuma dabbobinsu, baya ga karya gadoji da rusa gidaje da kuma wanke hanyoyin mota da ambaliyar tayi.

Jami’in yace a jimilce asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya 30 ruwan ya mamaye ya kuma hana amfani da su, baya ga lalata wasu sama da 200 a yankuna daban daban, abinda ya jefa rayuwar marasa lafiya da kuma mata masu juna biyu cikin hadari.

A bangaren ilimi, Banda yace makarantu 27 ambaliyar ta mamaye, kana kuma an mayar da wasu 18 sun zama matsugunin yan gudun hijirar da ruwan ya mamaye gidajensu, abinda ya hana yara komawa karatu.

Jami’in yace sun tattara wadannan alkaluma ne sakamakon wani aikin hadin gwiwar da suka yi tsakanin Hukumar UNICEF da wakilan gwamnatin Jihar Jigawa da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya, yayin da ya bayyana fargabar rashin abinci ga mutanen da iftila’in ya ritsda da su da kuma barazanar samun annobar kwalara saboda rashin tsaftaccen ruwan sha.

RFI

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories