Aisha Buhari ta nemi yafiyar ‘yan Najeriya

0
69

Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta ce saboda yawan burin da ‘yan Nijeriya suka ci a kan gwamnatinsu, ba ta da tabbacin ko sun biya wa ‘yan kasar bukatunsu da suka dauka a lokacin yaki neman zabe.

Aisha ta bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da ta yi da BBCi, ta bayyana cewar wannan dalili ne ya sa ta nemi afuwar mutanen kasar.

Ta bai wa ‘yan Nijeriya hakurin ne game da wahalar rayuwa da suke fuskanta yayin addu’o’i na musamman da ta shirya a ranar 1 ga watan Oktoba don bikin cika shekara 62 da samun ‘yancin kan kasa.

A lokuta da dama, an sha jiyo uwar gidan ta shugaban kasa, tana sukar gwamnatin tasu ko wasu masu ruwa da tsaki da ke cikin gwamnatin.

Lamarin da wasu shafaffu da mai ke ganin Aisha na yi musu hawan kawara.