HomeLabaraiAn yi wa dalibai 8,000 karin alawus din karatu a Nasarawa

An yi wa dalibai 8,000 karin alawus din karatu a Nasarawa

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Gwamnatin Nasarawa ta ce ta kammala shirin raba tallafin karatu na miliyan N218, ga dalibai  8,000 ’yan asalin jihar da ke karatu a manyan makarantun a ciki da wajen jihar.

Babbar Sakatariyar Hukumar Bayar da Tallafin Karatun, Hajiya Sa’adatu Yahya, ta ce tuni gwamnan jihar, Abdullahi Sule ya amince da fitar da fiye da miliyan N100 domin fara biya.

Ta ce za ayi rabon ne kashi biyu, kuma za a fara ranar 4 ga watan Nuwamba, a cibiyoyi daban-daban na jihar, kuma, “Da an kammala kashin farko na rabon ranar 4-ga wata.

“Kuma da zarar an mika wa gwamna duk takardun da suka kamata, za a fara biyan kashi na biyu.

“Ina kuma farin cikin sanar da daliban cewa sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi, an kara yawan kudin tallafin.

“Dalibai masu nazarin aikin lauya za su samu N300,000 madadin N100,000 da suka saba karba.

“Sai sauran daliban da ke karatun digirinsu na farko da za su karbi N20,000 madadin 10,000.

“Masu bukata ta musamman kuma za su karbi N30,000, a madadin N20,000.”

Ta kuma ce duk wannan karin da aka yi wa sauran bangarori da ke karatun Digiri na farko, zai fara aiki ne a wannan biyan, illa na masu nazarin aikin Lauya.

Jami’ar ta bayyana cewa dalili shi ne, sai bayan an saki kudin sannan aka amince da biyan su sabon tsarin.

Ta kuma ce za a fara tantance daliban da za su ci gajiyar daga karfe 9:00 na safe, zuwa 3:30 na yamma kullum, a sakatariyar mazabar Nasarawa ta Arewa, daga ranar 20-24, ga Oktoba.

Sai kuma ranar 25 zuwa 27 da za ayi a Nasarawa ta Yamma, yayin da a ta Kudu kuma za a yi ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga wata.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories