Hukumar kwastam ta sallami ma’aikata sama da 2,000

0
43

Hukumar Kwastam a Najeriya tace ta kori ma’aikanta sama da 2,000 a cikin shekaru 7 da suka gabata saboda aikata laifuffuka daban daban da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma taimakawa masu fasakauri.

Shugaban hukumar kanar Hameed Ali mai ritaya ya bayyana daukar wannan mataki mai tsauri lokacin da yake yiwa kwamitin majalisar wakilan kasar bayani, yayin da yace wasu daga cikin wadanda aka samu da laifi an kai su kotu, kuma ta daure su.

Ali yace daga cikin wadannan bara gurbin ma’aikatan da aka kora, wasu da dama sun taimaka wajen karkata kudaden harajin da hukumar ke samu domin biyan bukatun kansu, musamman abinda ya shafi kudin fiton motocin da ake shiga da su kasar.

Shugaban ya kuma bayyana cewar an dakatar da wasu daga cikin yan kasuwar dake kauce hanya wajen kin biyan harajin gwamnati, yayin da ya zargi wasu masu motoci wajen gabatar da takardun bogi akan motocin da aka kera a wannan shekarar, inda suke gabatar da takardun kera su a shekarar 2015.

Kanar Ali yace Najeriya bata da karfi da kudin da zata iya gina katanga akan iyakokin kasar, yayin da ya bayyana cewar kasar na fuskantar babbar kalubale ne akan iyakar ta da Jamhuriyar Benin saboda simogan da ake samu, amma ba iyakar Jmahuriiyar Nijar ba.

Babban jami’in yace ta hanyar amfani da fasahar zamani ne kawai za’a dakile matsalolin tsaron da ake da su akan iyakokin kasar.