Jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’addar da suka addabi mutane a hanyar Abuja-Kaduna

0
61

Dakarun Sojojin Nijeriya na rundunar Operation Whirl Punch, sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan da suka yi kaurin suna a kauyukan dake kusa daga kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a yakin da suke yi da ‘yan bindiga a jihar Kaduna.

Rahoton ya ce, dakarun da ke aiki da sahihan bayanan sirri, sun kai wani samame a yankin Abasiya-Amale da ke gabashin falwaya a karamar hukumar Kachia ta jihar inda suka fatattaki ‘yan bindiga.

A wannan bata kashin, sojojin sun yi galaba a kan ‘yan ta’addan inda daga bisani suka kona maboyarsu.

Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce sojojin na ci gaba da sintiri a yankin, Sojojin sun kwato gawarwakin ‘yan bindigar biyu da suka kashe a yankin.