HomeLabaraiZa mu taimaka wa Ukraine amma ba da makamai ba – Isra’ila

Za mu taimaka wa Ukraine amma ba da makamai ba – Isra’ila

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Ministan Tsaron Isra’ila, Benny Gantz ya ce Isra’ila ba za ta bai wa kasar Ukraine makamai ba domin yakar Rasha yayin da ake ci gaba da gwabza yakin na tsawon watanni takwas.

Yayin da kasar ke fuskantar hare-haren rokoki da jirage masu saukar ungulu, gwamnatin Isra’ila ta jajanta wa kasar Ukraine inda ta ce ba za ta iya taimaka wa kasar da aka yi wa kawanya da makamai ba.

Gantz, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake magana da tawagar jakadun Tarayyar Turai.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Ukraine ta ce za ta gabatar da wata bukata ta musamman da ta shafi tsaron sararin samaniyarta ga Isra’ila, domin taimaka mata da na’urori irin su Iron Dome, amma Gantz ya ce ba su shirya sayar da irin wadannan makamai ba.

Gantz ya ce: “Isra’ila tana goyon bayan Ukraine, NATO, da Yammacin Turai. Wannan shi ne abin da muka fada a baya kuma mun maimaita yau. Isra’ila na da manufar tallafa wa Ukraine ta hanyar taimakon jin kai, da kuma isar da kayan kariya na ceton rai.”

“Ina so in jaddada cewa Isra’ila ba za ta isar da na’urorin makamai zuwa Ukraine ba saboda la’akari da matakan da ake amfani da su,” In ji Gantz.

“Za mu ci gaba da tallafa wa Ukraine a cikin iyakokinmu, kamar yadda muka yi a baya,” in ji shi.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories