Zan daukaka kara kan hukuncin kotu da ta soke takarata – Aisha Binani

0
52

Sanata Aisha Binani, wadda ta lashe zaben fidda gwanin ‘yar takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, ta kuduri niyyar daukaka karar hukuncin kotu da ya soke nasarar da ta samu a zaben fidda gwanin jam’iyyar.

A wata tattaunawa da Binanin ta yi da Muryar Arewa a jihar, ta ce Nuhu Ribadu kamar dan uwa yake gare ta kuma yana da damar kalubalantar nasararta a kotu.

Binani ta ce ta dauki hukuncin na kotu a matsayin kaddara saboda a cewarta Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya so.

Ta bukaci magoya bayanta da kada su lalata katunansu na zabe saboda hukuncin kotu domin za ta daukaka kara.

“A matsayina na Kodinetar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Jihar Adamawa, zan tabbatar da samun nasararta a zabukan 2023 da ke tafe,” in ji Binani.

Idan za a tuna, a makon da ya gabata ne wata babbar kotu mai lamba 1 da ke Yola, karkashin mai shari’a Abdulaziz Anka, ta ayyana soke zaben fidda gwanin gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Adamawa saboda cewa jam’iyyar ba ta bi ka’idoji da kuma sharuda da aka gindaya mata ba yayin gudanar da zabukan fidda gwani.

Mai shari’a Anka ya kuma gargadi Binani da cewa ta daina daukar kanta a matsayin ‘yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar.