Buhari ya sanya hannu kan dokar habaka fasahar kere-keren cikin gida

0
46

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar habaka kere-keren cikin gida da zai taimakawa matasa masu hazakar kirkire-kirkire, shirin da ke kunshe da tsabar kudin zuba jari ga matasan har Naira biliyan 10 a wani yunkuri na karfafa gwiwar kere-keren cikin gida.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani a Najeriyar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami wanda ke sanar da wannan mataki a jiya labari lokacin da ya ke jawabi gaban dandazon manema labarai a Abuja fadar gwamnatin kasar ya ce sabuwar dokar za ta kuma bada damar kafa majalisar kula da masu fasaha da kuma kirkire-kirkire ta kasar.

A cewar Pantami sabuwar dokar ta samo asali ne saboda muradin gwamnatin kasar na samar da yanayin da ake bukata ga matasan Najeriya masu tasowa da masu kirkire-kirkire don magance kalubalen da suke fuskanta, wadanda suka hada da na karancin kudi da tsare-tsare masu inganci, da kuma karfafa gwiwa.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta ware naira miliyan dubu 10 wajen gudanar da shirin.

Farfesa Fantami ya ce bangaren fasahar sadarwar zamani na ba da gudummawar sosai wajen batun tattalin arzikin kasar, inda a wannan shekarar ya bada gudunmuwar kashi 18.42 bisa 100 na ma’aunin tattalin arzikin kasar, yayin da bangaren sadarwa da tattalin arzikin zamani ya bada gudunmuwar kashi 40 cikin dari.