HomeLabaraiBuhari ya sanya hannu kan dokar habaka fasahar kere-keren cikin gida

Buhari ya sanya hannu kan dokar habaka fasahar kere-keren cikin gida

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Shugaban Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar habaka kere-keren cikin gida da zai taimakawa matasa masu hazakar kirkire-kirkire, shirin da ke kunshe da tsabar kudin zuba jari ga matasan har Naira biliyan 10 a wani yunkuri na karfafa gwiwar kere-keren cikin gida.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani a Najeriyar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami wanda ke sanar da wannan mataki a jiya labari lokacin da ya ke jawabi gaban dandazon manema labarai a Abuja fadar gwamnatin kasar ya ce sabuwar dokar za ta kuma bada damar kafa majalisar kula da masu fasaha da kuma kirkire-kirkire ta kasar.

A cewar Pantami sabuwar dokar ta samo asali ne saboda muradin gwamnatin kasar na samar da yanayin da ake bukata ga matasan Najeriya masu tasowa da masu kirkire-kirkire don magance kalubalen da suke fuskanta, wadanda suka hada da na karancin kudi da tsare-tsare masu inganci, da kuma karfafa gwiwa.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta ware naira miliyan dubu 10 wajen gudanar da shirin.

Farfesa Fantami ya ce bangaren fasahar sadarwar zamani na ba da gudummawar sosai wajen batun tattalin arzikin kasar, inda a wannan shekarar ya bada gudunmuwar kashi 18.42 bisa 100 na ma’aunin tattalin arzikin kasar, yayin da bangaren sadarwa da tattalin arzikin zamani ya bada gudunmuwar kashi 40 cikin dari.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories