HomeLabaraiCikin kwanaki 2 rikicin kabilanci ya kashe mutane 150 a Sudan

Cikin kwanaki 2 rikicin kabilanci ya kashe mutane 150 a Sudan

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Akalla mutane 150 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu ciki har da tarin kananan yara bayan share tsawon kwanaki biyu ana bata kashi tsakanin Hausawa da kabilun da ke rayuwa a yankin kudancin jihar Blue Nile na kasar Sudan.

Rikicin wanda ya samo asali daga batun mallakar filayen noma da kiwo, shi ne mafi muni da aka fuskanta a baya-bayan nan tsakanin kabilun da ke zama a yankin na kudancin jihar Blue Nile.

An dai gwabza fadan na kwanaki 2 mai muni tsakanin kabilun a yankin Wad al-Mahi mai tazarar kilomita 500 da birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar inda shugaban yankin Abbas Moussa ya tabbatar da cewa a ranakun Laraba da Alhamis mabanbantan kabilun sun farwa juna lamarin da ya kai ga jikkatar mutane akalla 86 baya ga dimbin rayukan fiye 150 da da suka salwanta galibi Mata da yara da kuma tsofaffi.

Tuni dai al’ummar yankin suka fara wata zanga-zangar bukatar kawo karshen rikicin tare da kira ga gwamnatin kasar kan ta sauke gwamnan jihar wanda suke zargi da assasa rikicin.

Masu zanga-zangar rike d

Shirin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya yi gargadin yiwuwar fuskantar tashe-tashen hankula a yankin na Blue Nile sakamakon yadda makamai ke bazuwa a yankin wadanda ake shigar da su daga Habasha da kuma Sudan ta kudu dukkaninsu masu fama da yake-yake.

Babban jami’in Majalisar a Sudan Eddie Rowe ya ce tun farowar rikicin a ranar 13 ga watan nan akalla mutane 170 suka mutu yayinda wasu 327 suka samu munanan raunuka tsakanin kabilun biyu.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories