Jihar Kogi ta samu kason farko daga arzikin mai

0
50

Jihar Kogi ta shiga jerin jihohin da ke samar da mai a Najeriya inda tuni ta samu kasonta na rarar mai na farko daga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Kingsley Fanwo, shi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwar jihar a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Lakwaja.

Fanwo ya ce gwamnan jihar, Yahaya Bello ne ya sanar da hakan yayin taron nasu, inda ya ba da tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da samo wa jihar nasarori.

Gwamna Bello ya ce ko shakka babu fara samun kaso daga rarar man zai taimaka gaya wajen inganta rayuwar al’ummar Kogi.

Kwamishinan ya ce gwamnan ya nuna godiyarsa ga Shugaba Muhammadu Buhari da wannan cigaban da jihar ta samu.

Haka nan, ya ce Bello ya jaddada aniyarsa ta cika alkauran da ya yi wa ’yan jihar.