Najeriya na bukatar karin likitoci dubu 363 don bai wa jama’a kulawa

0
57

Shugaban kungiyar Likitocin Najeriya ta NMA Uche Rowland ya ce kasar na bukatar likitoci akalla dubu 363 domin kula da jama’ar kasar sama da miliyan 200, amma kuma har ya zuwa wannan lokaci kasar ba ta da likitocin da yawansu ya kai dubu 30.

Rowland ya ce abin takaici dubban likitocin kasar ne ke tserewa zuwa kasashen ketare domin samun rayuwa mai inganci ciki kuwa har da Birtaniya wadda ita kadai ke da yawan likitoci ‘yan Najeriya fiye da dubu 5 da 600.

Shugaban kungiyar likitocin ya ce a yankin kudancin Najeriya, likita guda na duba marasa lafiya akalla 30,000 shi kadai, yayin da a yankin arewa kuma likita guda ke duba marasa lafiya 45,000, sabanin likita guda akan marasa lafiya 600 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukata.

Rowland ya ce akwai yankunan karkarar da marasa lafiya kan yi tafiyar kilomita 30 kafin samun likitan da zai duba su saboda karancin jami’an kiwon lafiyar.

Alkaluman kungiyar sun bayyana cewar yanzu haka akwai likitoci akalla 40,000 da ke aiki a kasar, amma kuma wasu da dama na ci gaba da tsallakewa suna ficewa zuwa kasashen da suka ci gaba.