Dole ne ‘yan Najeriya su mallaki makaman kare kansu – T.Y Danjuma

0
59

Tsohon Ministan Tsaron Najeriya Janar T.Y Danjuma ya sake yin kira ga ‘yan kasar da su dauki makamai domin kare kansu da kansu daga hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ke satar mutane suna karbar kudin fansa, kalaman da a can baya suka  janyo masa bakin-jini a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bayan ya furta su a shekarar 2018.

Mista Danjuma ya bayyana cewa, ko dai da gan-gan sojojin Najeriya sun ki bai wa kasar kriya ko kuma dai kasar na cikin kawanya, yana mai bayyana bakin cikinsa kan kan yadda kasar mafi girmar kasar bakaken fata a duniya, ta fada hannun ‘yan ta’adda da ke cin karensu babu babbaka.

A matsayina na soja, babbar kariya ita ce, kaddamar da hari. A halin yanzu, dukkaninmu mun shantake. Wadannan  mutanen na dauke da makaman kare dangi, amma mu ba mu da su. Muna da yawa da fadin kasa. Suna son yi mana mulkin mallaka tare da kwace kasarmu. inji  Danjuma.

Mista Danjuma wanda ke magana a yayin mika sakonsa na ban-girma ga Manu Ishaku Adda Ali, sabon basaraken  Aku-Uka na 25 a Wukari na jihar Taraba a wannan Asabar, ya bayyana cewa, ba zai baiwa kowa makami ba, amma su tuntubi yadda mutane suka mallaki makaman domin bin hanyoyin da suka samu don kare kansu.

Kazalika ya ce, wannan kyakkyawar kasa da ake kiran ta Najeriya, na karkashin wasu miyagu ne da ke son kassaara ta, kuma watakila wasu daga cikinsu na nan tare da mu a cewarsa.

“Dole ne mu yi duk mai yiwuwa waje ceto kasar, in ba haka ba kuma, Najeriya ta kare” inji shi.