Ina da lafiyata takarar shugaban kasa zanyi ba kokawa ba – Tinubu

0
58

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Asabar, ya bayyana cewa shi ba shi da lafiya, sai dai ya daure, inda ya ce sau da yawa lamarin yakan ba shi mamaki yayin da ‘yan adawa ke nanata cewa ba shi da lafiya.

Tinubu ya bayyana haka ne a wajen liyafar cin abincin dare da kungiyar ‘yan kasuwar Kano suka shirya domin karrama shi.

Ya ce, “Ba gudun tseren nake yi ba na yadi 100 ko na yadi 500 ba kuma ina takarane a gasar dambe ba. kawai takarar shugaban kasa nake wanda aiki ne na ilimi.

“Ina da lafiyata sosai.”

Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC wanda manufarsa a Kano ita ce kaddamar da ofisoshin yakin neman zaben gwamna da shugaban kasa na jam’iyyar APC a birnin na kano ya sanar da bayar da gudummawar naira miliyan 500,000,000 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.