Karramawar shugaban kasa da yamin ta kara min kaimi – Sadiya Farouq

0
46

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq
ta bayyana jin daɗin ta bisa karramawar da ta samu ta NEAPS, inda ta ce abin zai ƙara mata ƙaimi da jajircewa a aikin ta.

Minista Sadiya ta ce: “Wannan wani muhimmin zango ne, musamman a rayuwa ta, domin wannan karramawa shaida ce ƙarara ta gamsuwar da aka yi da nasarorin da na samu a wajen ayyukan da na yi wa jama’a ya zuwa yanzu da kuma alhakin da aka ɗora mani a fagen ayyukan inganta rayuwa da jinƙai a cikin ‘yan shekarun nan.

Daga nan sai ta bayyana cewa “ina so in ƙara miƙa matuƙar godiya ga mai girma Shugaban Ƙasa saboda damar da ya ba ni na yi wa ƙasa ta aiki a matsayin Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, sannan ta hanyar wannan muƙamin na yi ƙoƙarin bautata wa ɗimbin mutane marasa galihu waɗanda ke cikin buƙatar a inganta rayuwar su da taimakon jinƙai cikin gaggawa a faɗin ƙasar nan.

“Haka kuma ina godiya matuƙar gaske ga kamfanin ‘TBS Media’ da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya da su ka ga dacewa ta har su ka ba ni wannan babbar kyauta ta NEAPS ta shekarar 2022 a ɓangaren ayyukan jinƙai, kuma su ka ɗora ni kan matakin shiga da’irar sauran manyan ‘yan Nijeriya waɗanda su ma aka karrama su tare da ni a yau.”

Ministar ta sha alwashin za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarin ta wajen yi wa ƙasar nan aiki wanda yin shi ne gudunmawar ta wajen taimakawa a tsamo Nijeriya daga cikin matsalolin da su ka addabe ta.

Mai taimaka wa ministar a fagen aikin jarida, Nneka Ikem Anibeze, ta yi ƙarin bayanin cewa wannan kyautar karramawa da aka yi saboda aiki ga jama’ar Nijeriya “manufar ta ita ce a karrama muhimman ayyukan da aka yi wa jama’a a Nijeriya ta hanyar gudunmawar da jama’a ɗaiɗaiku da jihohi da mutanen unguwa su ka bayar wajen shugabanci da aikin jama’a da jinƙai.”

In dai ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranci miƙa waɗannan kyaututtuka ga Minista Sadiyya da wasu mutum 44.