HomeLabaraiMazauna Abuja sun koka kan karin kudin wutar lantarki

Mazauna Abuja sun koka kan karin kudin wutar lantarki

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Mazauna wasu unguwanni a Abuja na barazanar yin zanga-zanga sakamakon tsawwala musu kudin wutar lantarki.

Daga cikin wadanda suka koka har su ka yi barazanar sun hada da mazauna unguwar Mararraba da ke Karamar Hukumar Karo ta Jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja, babban birnin Najeriya.

A hirar da NAN ta yi da wasu mazauna unguwar sun ce, takardar biyan kudin wutar da aka kawo musu na watan Agusta da kuma Satumba na wutar da suka sha, ya wuce hankali.

Wani mai suna Mista Richard Ekoja wanda ke Marraba a karkashin ofishin hukumar rarraba wutar lantaraki ta AEDC, ya ce, ta ba shi takardar biyan kudin wuta na Naira 22,269,70

Na watannin Agusta da Satumba, a maimakon Naira 6,000 da 9,000 da ya saba biya a baya.

“Ban ga dalilin da kamfanin AEDC zai bukaci in biya wannan makudan kudi ba, a cikin irin wannan halin da kasar nan ta ke ciki na fama da rashin sukuni ba,” in ji Richards

Shi kuwa Mista Leonard Ogwuche cewa ya ke wannan cuta ce karara, saboda idan wani abu ya lalace a tiransifoma, ko waya, ko turakun wutar lantarkin, su suke harhada kudi su saya, don haka ba za su yarda ba.

Wani jami’in kamfanin da aka yi hira da shi, cewa ya yi, babu gudu, babu ja da baya a karin, saboda su ma haka suke sayen wutar da tsada.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories