PDP sai ta yi nasara a Anambra – Okowa

0
46

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa ya ce jam’iyyarsa za ta yi nasara a jihar Anambra, a zaben 2023.

Duk da rinjayen jam’iyyar APGA, wadda ita ma ke da dan takarar shugaban kasa, da kuma jam’iyyar Labour Party, LP, wadda dan takararta, Mista Peter Obi ya fito daga jihar, Okowa ya ce PDP za ta karbe jihar.

Okowa wanda abokin takarar Atiku Abubakar ne ya samu wakilci a Onitsha a bikin Ofala karo na 20 na basaraken gargajiya na tsohuwar masarautar Obi Alfred Nnaemeka Achebe, wanda jagoran kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Anambra, Farfesa Obiora Okonkwo, shugaba United Nigeria Airline.

Okonkwo wanda ya zanta da manema labarai yayin da yake wakiltar Okowa ya ce: “PDP ta shirya tsaf don yakin neman zabe. Anambra ta kasance gidan PDP, kuma kuna iya duba ta. A baya dai mun samu gagarumin rinjaye a dukkan zabukan shugaban kasa, kuma kusan a kowane lokaci mun samu rinjayen zaben ‘yan majalisun tarayya, kuma bana tunanin hakan zai bambanta.

“Ba ni da tantama cewa a karshen wannan rana, mutanen Anambra za su san cewa muna bukatar a sake hada mu da Abuja, kuma waya daya da za ta ba mu wannan alaka da harkar siyasa ita ce PDP.”

Da yake magana kan mamayar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA a jihar Anambra, Okonkwo ya bayyana APGA a matsayin kawar PDP.

“APGA ita ce ke rike da jihar a lokutan baya lokacin da PDP ta samu kashi 95 na kuri’un jihar, a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar Anambra. Ina ganin haka zai kasance.

“Mutanen Anambra sun kasance suna zabar PDP a kowane lokaci, kuma ina mamakin dalilin da ya sa kuke jin wannan lokacin zai bambanta. Muna da yakinin cewa za mu ci zabe a Anambra.”