An tsaurara tsaro a Abuja bayan gargadin harin ta’addanci

0
42

Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCTA) ta kara tsaurara matakan tsaro a Abuja, biyo bayan sanarwar barazanar kai hari da Ofishin Jakadancin Amurka ya yj.

Ma’aikatar ta shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro suna aiki tukuru domin tabbatar da doka da oda.

A wata sanarwa da Daraktan yada labarai Muhammad Sule ya fitar, ta ce an yi shirye-shiryen da suka dace don kare rayuka da dukiyoyi.

Kakakin ya sanar da cewa Ministan babban birnin tarayya, Muhammad Bello ne ya jagoranci wani taron gaggawa a ranar Litinin.

Bello ya bukaci jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen kare mazauna birnin tarayya Abuja daga hare-hare.

Sai dai hukumar ta FCTA ta karyata rade-radin cewa an rufe wasu makarantu.

Bello ya shawarci mazauna yankin da su bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar ba da sahihan bayanai masu inganci kuma a kan lokaci.

Ma’aikatar ta bukaci mazauna yankin da masu ziyara da su gudanar da ayyukansu na yau kullum kamar yadda suka saba.

Sanarwar ta kara da cewa, “An tattara jami’an tsaro gaba daya don duba duk wani nau’i na hana shigowa FCT”.

Har ila yau, a ranar Litinin, rundunar ‘yansandan Nijeriya ta sanar da wani atisayen yaki da ta’addanci mai suna “Operation Daukin Gaggawa”.

Za a gudanar da atisayen ne a hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Talata da Laraba.

Al’umma da dama mazauna Abuja sun shiga rudani tun bayan fitar sanarwar barazanar kai hare-haren da aka ce ‘yan ta’adda na shirin kai wa.