Bazoum ya kaddamar da aikin gina samar da wutar lantarki a Kandaji

0
78

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed, ya kaddamar da fara aikin gina sashen da zai samar da wutar lantarki a madatsar ruwan Kandaji wanda ake saran ya samar da megawatt 600 na hasken wuta ga kasar.

Shidai wannan gagarumin aikin samar da wutar lantarki zai ci Dala biliyan guda da miliyan 100 wajen kammala aikin gina madatsar ruwan da zata samar da wutar lantarkin wanda za’a dauka daga kandaji zuwa birnin Yammai.

Tuni Bankin raya kasashen Musulmi na IDB ya zuba sama da Cefa biliyan 55 a cikin aikin, wanda ake saran a gina turakun da zasu dauki wutar da zata ratsa birane da garuruwan dake tsakanin Kandaji da Yammai.

Shi wannan madatsar ruwa na Kandaji, ana sa ran cin moriyarsa ta bangarori da dama da suka hada da noman rani a kadada dubu 45 da samar da ruwan sha tare da hasken wutar lantarki.

Ana saran wannan aiki zai taimaka wajen bunkasa rayuwar jama’ar dake wadanann yankuna, musamman ta bangaren tattalin arziki da ilimi da kuma kula da lafiyarsu.