Sojin Najeriya sun kame tarin ‘yan ta’adda da ke shirin kai hare-hare sassan kasar

0
55

Rahotanni na cewa dakarun Sojin kasar nan sun kame tarin ‘yan ta’adda da masu taimaka musu a wasu jerin sumame da suka gudanar cikin biranen Abuja da Kano, kwana guda bayan gargadin kasashen Amurka da Birtaniya na yiwuwar fuskantar hare-haren ta’addanci a kasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wata majiya ta tabbatar mata da kaddamar da mabanbantan sumamen da ya kai ga kame tarin ‘yan ta’adda a cikin birnin Abuja fadar gwamnati da kuma wasu yankuna bayan samun bayanan sirri game da maboyar ‘yan ta’addan da kuma shirinsu na kaddamar da munanan hare-hare.

Jaridar ta ruwaito cewa tuni aka kame tarin ‘yan ta’adda a birnin na Abuja da kuma sumamen Sojin a arewacin jihar Borno da ke kan iyakar kasar da Chadi da Nijar da kuma Kamaru baya ga yankin Alagarno da kuma cikin dajin Sambisa baya ga dazukan jihohin Katsina da Kaduna da Zamfara wanda aka yi nasarar bankado maboyar ‘yan ta’adda da dama tare da kamesu.

A cewar jaridar tun gabanin gargadin ofishin jakadancin Amurka jami’an tsaron na da masaniya kan barazanar ‘yan ta’addan wadanda ke yunkurin kitsa munanan hare-hare a sassan kasar.

Akwai dai majiyoyin da ke cewa da dama daga cikin kwamandojin ISWAP yanzu haka sun saje da fararen hula a birnin Abuja don kai farmaki, a wurare daban-daban dalilin da ya sanya ofisoshin jakadancin kasashe fitar da sanarwar gargadi ga al’ummominsu da ke rayuwa a Najeriya.

Majiyar ta ce makwanni 2 da suka gabata sai da jami’an tsaron suka kame wasu manyan ‘yan ta’adda 3 da suka yi basaja da nufin sajewa da fararen hula a a unguwar baya ga Abubakar Dan Borno da DIA ta kame a mararraba cikin makon jiya.

Jaridar ta Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan ta’adda da dama sun tattaru a biranen Abuja da Kano kuma jami’an tsaron na aiki tukuru don bankado maboyarsu.