Wata kungiyar kiristoci ta yi mubaya’a ga Tinubu da Shettima

0
68

Yayin da batun tsayar da Musulmi da Musulmi a takarar shugabancin Najeriya da jam’iyyar APC ta ke ci gaba da jan hankula, wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke goyon bayan APC ta sha alwashin ba da gudunmawa ga takarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023.

Ƙungiyar ta Christian Northern Najeriya Political Forum ta yi haka ne duk da irin adawar da Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ke yi da wannan lamari.

Shugabannin ƙungiyar sun bayyana goyon bayan nasu ne a Kaduna a wani taro da suka yi da wasu jagorori na jam’iyyar.

Haka kuma ƙungiyar ta ce ta yi haka ne a ƙoƙarin da take yi na kauce wa duk wani tarnaki da ka iya kawo cikas ga ɗan takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin inuwar APC  a zaɓen 2023.