Matashin dan kasuwa mai shekaru 23 ya zama jakadan zaman lafiya

0
108

Wani dan kasuwa mai shekaru 23, Nlemchukwu Onyedikachi, an ba shi lambar yabo ta jakadan zaman lafiya, a wani taron da ake ci gaba da gudanarwa mai taken, “Gudunwar da matasan Najeriya, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma, kafafen yada labarai da tsaro za su taka a babban zaben 2023.

Onyedikachi, Babban Jami’in kamfanin KachiPlug Nigeria ne, an karrama shi ne saboda irin nasarorin da ya samu a matsayin mai neman zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Shugaban kula da ayyuka na PAIA, Mista Kingsley Amafibe, ya bayyana cewa bugu na bana yana da hadin gwiwa da Jami’ar Gudanarwa ta Amurka, Amurka, ya kara da cewa akwai bukatar inganta zaman lafiya a matsayin kayan aiki mai kyau na ci gaban al’umma.

Da yake jawabi a taron da aka yi a Abuja ranar Talata, Onyedikachi ya ce yana alfahari da samun kyautar.

Ya ce, “Ina jin dadin samun wannan lambar yabo tare da wasu mutane a fadin duniya wadanda suka ba da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya a fadin Nijeriya.

“Duk da haka, ina kira ga kowa da kowa ya lura cewa zabukan 2023 masu zuwa na da muhimmanci ga zaman lafiya da hadin kan al’ummar kasa, kuma ya kamata dukkan hannaye su tashi.”