Masanin tattalin arzikin, duk wadannan matsaloli ne da za a iya fuskanta saboda takaitaccen lokacin da aka bayar na mayar da wadannan kudade.

Aliyu Da’u, ya ce,” Baya ga wadannan matsaloli, akwai kuma fargabar da mutane ke da ita cewa batun sauya kudaden nan zai iya durkusar da jarin wasu musamman ‘yan kasuwa.”

Ya ce, to amma tun da CBN ya ce a mayar da kudin don sauyawa, to ba mamaki akwai wasu bayanai na sirri da gwamnati ke da shi wanda jama’ar gari ba su dashi, kamar batun ‘yan siyasar da suka tara kudi suka ajiye don ayi amfani da su a lokacin zabe.

To ba mamaki an bayar da wannan takaitaccen lokaci ne don a samu damar karbe kudaden daga wajen ‘yan siyasa wata kila a samu saukin raba kudi a loakci zabe.

 Masanin tattalin arzikin ya ce, bayan siyasa akwai kuma batun ‘yan bindiga d ake satar mutane don kudin fansa, ba mamaki suma suna da irin wadannan kudade da za a sauya, to idan har aka bayar da wannan wa’adi ai dole su rabu da su don sauyawa.

 Ya ce, to idan aka yi la’akari da irin wadannan misalai, a iya cewa matakin sanya wa’adin ya yi dai-dai, to amma kuma a hakikanin gaskiya lamarin zai shafi mutane sosai musamman ‘yan kasuwa.

 A ranar Laraba ne babban bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar daga takardar naira 100 zuwa 1000, in da ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.

 Kazalika CBN din, ya ce sabbin kudaden da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022, sannan kuma za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023.