Macron ya sha alwashin kara shekarun ritaya da akalla shekaru 3

0
51

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sha alwashin kara shekarun ritaya a kasar da akalla shekaru 3 don baiwa matasa damar daukar lokaci mai tsayi suna bayar da gudunmawa.

A wata zantawarsa da gidan talabijin din France 2, Macron ya ce za a fara amfani da tsarin daga shekara mai zuwa inda ya ce lura da yadda Faransawa ke da tsawon rai abu mafi muhimmanci shi ne a baiwa matasa damar bayar da cikakkiyar gudunmawa a lokaci mai tsayi.

Macron ya bayyana cewa daga shekarar 2031, shekarun ritaya mafi karanci za su rika faraway daga shekaru 62 zuwa 65 wanda zai baiwa ma’aikaci damar samun cikakken kudin fansho da sauran hakkokinsa.

Shugaban na Faransa ya ce zai yi wata tattaunawa da kungiyoyin kwadago don cimma jituwa kan kudirin nasa wanda tuni ya samu maraba daga wasu ma’aikatan yayinda wasu suka fara suka akai.

Sabbin matakan karin shekarun ritayar dai zai shafi bangarorin ma’aikatan da suka yi matukar cancanta yayinda wadanda suka gaza cimma ka’idojin aiki da kuma Mata wadanda rainon yara da kula da gida ke katse ayyukansu za su fara aiki har zuwa shekaru 67.