Na ɗauki ciki duk da ƙwayar tsarin iyali da nake sha

0
67

Lokacin da Susan Wamaitha ta fara jin rashin lafiya shekara ɗaya da ta wuce, ta zaci matsaloli ne da ƙwayoyin hana ɗaukar ciki suke haifarwa waɗanda ta sha wata ɗaya kafin haka, amma sai aka gano tana ɗauke da ciki har sati takwas.

Matar mai shekara 32 yanzu tana da ‘ya’ya uku. Abin da ba ta sani ba shi ne, an haramta amfani da ƙwayar da ta fara sha a watan Yunin 2021 a Kenya.

Sunan da aka fi sanin ƙwayar da shi a Kenya shi ne “Sofia” amma a China ake yin ta, sannan kuma an rubuta dukkan bayanan da ke jikin kwalin maganin da

Sunan da aka fi sanin ƙwayar da shi a Kenya shi ne “Sofia” amma a China ake yin ta, sannan kuma an rubuta dukkan bayanan da ke jikin kwalin maganin da Chinanci.

Ciwon kai da yawan amai

“Ban san an haramta amfani da ita ba. Ƙawayena da yawa na amfani da ita ba tare da wata matsala ba,” kamar yadda Wamaitha ta faɗa wa BBC.

Kamar sauran mata a Kenya, ta fara amfani da ƙwayar ce saboda sauƙin kuɗi da kuma sauƙin amfani saboda ana shan ta ne sau ɗaya a wata.