Nnamdi kanu ya nemi diyyar biliyan 100 kan ci gaba da tsare shi da gwamnatin tarayya ke yi

0
62

Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ya shigar da karar gwamnatin tarayya a gaban kotu kan ci gaba da tsare shi da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ke yi.

A karar da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, Kanu na neman a gaggauta sakin sa daga hukumar DSS tare da biyansa diyyar Naira biliyan 100 saboda tauye hakkinsa na ‘yanci da mutuncin dan Adam.

Kanu ya ce karar ta zama dole ne biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya na yin biyayya ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 13 ga Oktoba, wanda ya yi watsi da tuhumar ta’addancin da ake yi masa.

Kotun, wadda Mista Mike Ozekhome, SAN, ya shigar a madadin Kanu, mai kwanan wata 21 ga Oktoba na dauke da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1945/2022.

Kanu ya ce an yi shari’ar ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin 1999.