Sojojin Amurka sun kai samame wani rukunin gidaje a Abujan Najeriya

0
50

Sojojin Amurka da jamiā€™an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, sun kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke unguwar Lugbe a babban birnin tarayya Abuja.

An kai farmakin ne a daidai lokacin da ake kara tada jijiyoyin wuya kan yiwuwar harin ta’addanci a babban birnin kasar.

Amurka da Birtaniya sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja, musamman kan gine-ginen gwamnati da wuraren ibada da makarantu da dai sauransu.

Gwamnatocin Australia, Ireland da Canada suma sun nuna fargaba kan yiwuwar barazanar harin ta’addanci a babban birnin Najeriya.

A yayin farmakin da aka kai a rukunin gidaje na Trademore, an takaita zirga-zirga gaba daya, yayin da jamiā€™an tsaro ke farautar masu tayar da kayar bayan.

Wata sanarwa da hukumar gudanarwar rukunin gidajen ta fitar, ta bukaci mazauna yankin da su kasance cikin taka tsan-tsan.

Rahotanni daga Najeriya sun ruwaito yadda jamiā€™an tsaro ke bakin kokarinsu wajen ganin an dakile munanan hare-haren da ā€˜yan taā€™adda masu biyayya ga kungiyar IS a yammacin Afirka ta ISWAP suke kokarin kaiwa Abuja da kewaye.

An gano shigar ā€˜yan taā€™addan Abuja ya biyo bayan wani gagarumin aikin leken asiri ta sama da samamen da sojojin Najeriya suka yi a yankin arewa mai nisa na Borno mai iyaka da Chadi da Nijar da Kamaru da dazuzzukan Alagarno da Sambisa a Arewa maso Gabas, da kuma hare-haren bama-bamai a yankunan da ke da dazuzzuka a sassan kasar.