Elon Musk ya kammala sayen Tuwita

0
45

Fitaccen attajirin nan a duniya Elon Musk, ya kammala yarjejeniyar dala biliyan 44 domin siyan kamfanin Tuwita bayan watanni da aka shafe ana ce-ce-kuce.

Rahotanni sun ce shugaban kamfanin Parag Agrawal, na daga cikin manyan jami’an kamfanin da aka sallama daga aiki. Rahotanni sun ce mutane da dama za su yi matukar farin ciki da sallamar Prag Agrawal, Kuma wannna wata alama ce da Elan Musk, ke nunawa na cewa shi ne mai cikakken iko.

Daman an ji haushin yadda aka haramtawa tsohon shugaban Amurka Donald Trump, amfani da shafin na Tuwita.

Elon Musk, ya ce yana son ya sayi kamfanin na Tuwita ne saboda jama’a ba don ya yi kudi ba.

Wata yar jarida da ke aiki da jaridar Washington Post ta Amurka ta bayyana yadda za a samu sauye sauye bayan mr Musk ya mallaki kamfanin sada zumuntar na Tuwita.

Tace ina gani yakamata a shirya dawowar Donald Trump, cikin masu amfani da wannan shafi.

“Ina mai tabbatar da cewa hakan zai faru wata rana.Sannan kuma ina gani shi ba mutum ne wanda ke son hadin kai wajen yanke hukunci ba, mutum ne wanda ke son yanke hukunci da kansa da kuma son nuna iko a kan abubuwa da dama.Kuma ina ganin dole mu tsammaci ganin karin kalaman kiyayya a wanann shafi.Kodayake Musk ya yi alkawarin cewa ba za a samu hakan ba, to sai mu zuba ido mu gani.”

 Yunkurin Elon Musk, na sayen shafin Tuwita ya janyo zazzafar muhawara kan makomar shafin – gwamnatin Amurka ma ta nuna damuwa kan tasirin da kafofin sada zumunta ke da shi.

Sai dai bukatar Musk ta sayen Tuwita kan $44bn ya ci gaba da jan hankali musamman kan tarihin irin wallafe-wallafe da hamshakin mai kudin yake yi.