MDD ta rabawa daruruwan ‘yan gudun hijira gidaje a jihar Borno

0
39

Majalisar Dinkin Duniya ta samar da gidaje 804 ga ‘yan gudun hijirar da suka rasa muhallansu a jihar Borno, tare da raba gidajen ga iyalan da rikicin masu tayar da kayar baya ya daidaita.

‘Yan gudun hijira da dama ne suka barke da murna bayan da shirin raya kasa na majalisar dinkin duniya wato UNDP ya samar musu da gidajen, tare da tallafin gwamnatin kasar Jamus.

Wannan dai wani shiri ne karkashin MDD na daidaita rayuwa ga mutanen da rikicin Boko haram ya tagayyara a yankin tafkin Chadi.

Daruruwan ‘yan gudun hijira gwamnati ta mayar da su gida, bayan tabbatar da cewa tsaro ya inganta a garuruwansu.

Hukumomi na duniya na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda rikice-rikicen masu dauke damakamai ke ci gaba da jefa mata da kananan yara cikin mummunan yanayi, musamman a kasashen Afirka.