HomeLabaraiBabu inda aka dasa bom a Abuja - Rundunar ‘yan sanda

Babu inda aka dasa bom a Abuja – Rundunar ‘yan sanda

Date:

Related stories

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Bankuna zasu cigaba da karbar tsofaffin kudi ko da bayan karewar wa’adi – Emefiele

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce Bankuna...

Cacar-bakin da ya barke tsakanin PDP da APC kan abun da ya faru yayin zuwan Buhari Kano

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da babbar jam’iyyar adawa...

Rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa an dasa bama-bamai a birnin.

Bayanin haka ya fito ne ta sanarwar da kakakin rundunar, Oluyiwa Adejobi ya fitar yana gargdin jama’a da su kiyayi yada jita-jita marar tushe ballantana makama.

“Muna masu kara jaddada cewa yankin babban birnin tarayya na cikin zaman aminci, kuma babu wata barazana ga lafiya ko dukiyar kowa,” in ji Kakakin.

Sannan ya yi kira ga jama’ar da ke ciki da kuma wajen yankin da su yi watsi da wannan labari na karya da ake yadawa don kawai a firgita jama’a.

Ya kuma ce, rundunar ’yan sandan na ci gaba da daukar matakan tsaron da suka kamata an kawar da duk wasu ayyuka na bata gari a kasa baki daya.

Hankulan jama’a a Najeriya ya tashi matuka tun makon da ya wuce sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar na cewa za a kai wa babban birnin harin ta’addanci.

Ofisoshin jakadancin kasashe da ke birnin sun gargadi ’yan kasarsu kan sanarwar ta Amurka, tare da umarnin su da kiyaye.

Shugaba Buhari ya kwantar wa ’yan kasa hankali kan lamarin, yana cewa jami’an tsaro na aikinsu yadda ya kamata don kawar da duka wata barazana ga birnin da ma kasa baki daya.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories