Kotun daukaka kara tace a ci gaba da tsare Nnamdi Kanu

0
44

Kotun daukaka kara da ke Abuja, ta amince da dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke na gurfanar da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu bisa zargin ta’addanci.

Gwamnatin Tarayya, ta yi ikirarin cewa an sallami Kanu, amma ba a wanke shi ba, kuma ta garzaya kotu domin ta dakatar da aiwatar da hukuncin sakin.

Kotun daukaka kara ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke wanda ya shafi mayar da Kanu daga Kenya zuwa Najeriya tare da ajiye tuhumar da ake masa na ta’addanci.

A ranar Juma’a ne kwamitin alkalai mai mutane uku karkashin jagorancin mai shari’a Haruna Tsamani ya bayyana cewa zai dace a jira karar zuwa gaban kotun koli.