HomeLabaraiMahara sun kone gidaje 10, sun kwashi abinci a kauyen Kano

Mahara sun kone gidaje 10, sun kwashi abinci a kauyen Kano

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Maharan da ba a sansu ba sun kai farmaki a Dan Jamfari ta kauyen Barbaji da ke Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano.

Wani mazaunin kauyen mai suna Magaji Audu ya ce, maharan da yawansu ya kai kimanin 200 dauke da muggan makamai sun shigo kauyen ne da tsakar dare.

“Sun shigo ne dauke da sanduna da adda suna bi gida-gida wai su na neman wani babur da aka sace.

“Sun yi kokarin su sare ni a gaban iyalina idan ban fito musu da ’ya’yana ba, wadanda suka ce sun sace musu babur,” in ji Malam Audu.

Ya ce, bayan nan ne sai suka dawo washegari da dare a inda suka sa wa gidansa wuta, iyalansa suka gudu.

Maharan kuma suka shiga kwashe kayan abinci da kaji da talotalo da sauran kayan noma bayan su kone gidaje 10 a kauyen.

Hakimin Rogo Alhaji Muhammadu Maharazu ya tabbatar wa da Vanguard  afkuwar lamarin.

Hukumar agajin gaggawa ta Jihar Kano ta kai wa mutanen kauyen kayan agaji a ranar Juma’a.

Shugaban karamar hukumar Dakta Saleh Jilli ya ce, gwamanti za ta zagulo wadanda suka aikata wannan zalunci ta kuma hukunta su.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories