HomeLabarai‘Yan sanda sun cafke kasurgumin dan bindiga a Jigawa

‘Yan sanda sun cafke kasurgumin dan bindiga a Jigawa

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Abdulkadir Alhassan mai shekaru 42 da haihuwa wanda ya dade yana ta’addanci a jihar da kuma Jihar Kano.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Talata a kauyen Sabon Sara da ke karamar hukumar Ringim.

Shiisu ya bayyana cewa wanda ake zargin kasurgumin dan fashi da makami ne kuma mai garkuwa da mutane wanda aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifukan fashi da makami.

“Wanda ake zargin an bada belinsa kwanan nan a kan laifin hada baki da kuma aikata fashi da makami a kotun majistare Babura,” in ji shi.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama daga jihohin Jigawa da Kano.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin karbar miliyoyin Naira daga iyalan wadanda abin ya shafa a matsayin kudin fansa.

Kakakin ‘yansandan ya kara da cewa wadanda ake zargin ya bayyana sunan wani dan kungiyarsu mai suna Alhassan Ya’u dan shekaru 45 a kauyen Dogamare da ke karamar hukumar Ringim.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories