‘Yansanda sun fatattaki ‘yan bindiga, sun ceto mutane 21 da shanu 20 a Katsina

0
141

Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina a ranar Asabar, ta ce ta dakile harin da wasu ‘yan bindiga da suka kai inda suka ceto wasu mutane 21 da aka yi garkuwa da su tare da kwato shanu 20 da aka sace.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Gambo Isah, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa a ranar Asabar, kuma nan take kwamishinan ‘yansandan ya bayar da umarnin daukar matakin gaggawa yayin da jami’an rundunar suka bi sahun ‘yan bindigar a kewayen Buraji da kauyukan Sabon Sara.

A cewarsa, kwamandan yankin na Dutsinma, ACP Mohammad Makama, ya jagoranci tawagar ‘yansanda masu fikira, inda suka tare hanyar fitar kauyen Gandun Sarki, inda suka yi artabu tare da samun nasarar kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su tare da kwato shanun da aka sace.

Ya ce an kashe ‘yan bindiga da dama, wasu kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kai rahoton duk wani motsi da suka samu da kuma wadanda suka samu raunukan harbin bindiga ga ‘yan sanda domin a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kuliya.