Ghana za ta ja ragamar kwamitin tsaro na majalisar dinkin Duniya

0
49

Ghana ta shirya tsaf don darewa kan kujerar shugabancin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata, 1  ga watan Nuwamban wannan shekarar.

Shugabancin wannan kwamitin, wanda wa’adinsa wata guda ne kacal, zai bai wa Ghana damar jan ragamar muhawwarorin da za a yi, wadanda ke da nasaba da zaman lafiya da tsaron duniya.

Ana sa ran shugaban Ghana, Nana Akufo Ado da kuma ministan harkokin wajen kasar su kasance a birnin New York na Amurka don halartar taron.

Kwamitin tsaron yana da mambobi 15 ne,kuma shi ke da alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.