Shugaba Muhammadu Buhari zai yi taron gaggawa da manyan jamiāan tsaron kasar a Abuja a ranar Litinin.
Wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce taron zai mayar da hankali ne kan yadda za a karfafa matakan tsaro a sassan kasar.
Najeriya, wacce ita ce kasar da ta fi yawan alāumma a nahiyar Afirka, na fama da matsalar hare-haren āyan bindiga da Boko Haram a Arewaci da kuma matsalar āyan aware a Kudanci, ko da yake mahukuntan kasar sun ce lamarin na lafawa.