HomeLabaraiMutane 60 sun mutu sakamakon ruftawar gada a India

Mutane 60 sun mutu sakamakon ruftawar gada a India

Date:

Related stories

Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa...

Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano...

Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim...

Hukumomin kasar India sun ce akalla mutane 60 suka mutu lokacin da wata gadar da ta kwashe shekaru sama da 100 ana amfani da ita ta rushe, yayin da wasu da dama kuma suka fada ruwa.

Ministan dake kula da Yammacin jihar Gujerat, Brijesh Merja ya tabbatar da mutuwar mutanen 60 sakamakon hadarin, yayin da yace kuma anyi nasarar ceto mutane sama da 80 da ransu.

Hukumomin sun ce akalla mutane kusan 500 ke kan gadar lokacin da ta rufta sakamakon sakewar da robobin dake rike da ita suka yi, cikin su harda mata da yara.

Ita dai wannan gadar ba’a dade da kammala gyaranta ba, kuma tana garin Morbi ne dake da nisan kilomita 200 daga Ahmedabad a Jihar Yammacin Gujerat.

Kafofin yada labaran kasar sun ce mutanen da suka taru akan gadar suna gudanar da ibada ne akan kogin Machchhu, yayin da wasu kafofi suka nuna hotunan bidiyon da ake bayyana cewar na hadarin ne dauke da mutanen dake kokarin yin fito domin tsira da rayukansu.

Kamfanin talabijin na NDTV yace an bude gadar ne ba tare da samun takardar inganci daga hukumomin dake kula da aikin ba.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories