An cafke wasu da ake zargi da hannu a mutuwar mutane sama da 130 a Indiya

0
51

‘Yansanda a Kasar Indiya sun sanar da kama mutane tara da ake zargin suna da hannu wajen rushewar gadar da aka samu a Jihar Gujerat wadda ta kashe mutane sama da 130.

Wani babban jami’in ‘yansandan yankin, mai suna Ashok Kumar Yadav, ya ce mutanen tara da aka kama, na daga cikin ma’aikatan kamfanin da ke kula da gadar a Morbi, kuma yanzu haka ana gudanar da bincike a kansu domin ganin ko za a tuhume su da laifin aikata kisan kai.

Daruruwan baki ne suka taru a kan gadar domin gudanar da bikin addini da ake kira Diwali, yayin da hotunan bidiyon da aka nada suka nuna yadda gadar ke motsawa daga bangare zuwa bangare kafin ruftawarta.

Wani da ya tsallake rijiya da baya, Madhvi Ben ya ce suna tsaye a kan gadar lokacin da ta katse, abin da ya kai ga mutane yin ihu da kuma neman tsira da rayukansu.

Shugaban ‘yansandan yankin, P. Dekavadiya ya ce adadin mutanen da suka mutu a hadarin wanda ya faru a jihar Firaminista Narendra Modi ya kai 137, kuma akwai yara 50 da jariri dan wata biyu da shi ma ya mutu.

Wani dan majalisar yankin, Kalyanji Kundariya, ya ce iyalansa 12 ne cikin wadanda suka mutu a hadarin.