Gwamnan Kebbi ya umarci a biya biliyan 2 kudin hutun ma’aikata

0
46

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya ba da umurnin fitar da Naira biliyan 2.5 domin biyan kudin hutun shekaru biyu na shekarar 2021 da 2022 na ma’aikatan jihar da kananan hukumomi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan kudi na jihar, Ibrahim Muhammad Augie, ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi ta hannun mai ba gwamna shawara kan harkoki yada labaru, Yahaya Sarki.

A cewar sanarwar, “Gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancin, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta saba biyan bukatun da ya rataya a wuyanta na ma’aikatanta da masu ritaya.”

Hakazalika, sanarwar ta ci gaba da cewa, Jihar Kebbi na daga cikin jiga-jigan jihohin da suka fi kowa samun walwala da ci gaban ma’aikata, “Dukkan albashi, fansho, giratuti, kudaden hutu, karin girma, ci gaba da horarwa gwamnati na biya kankari da kuma kula da su akai-akai tun daga shekarar 2015 zuwa yau.”

Kwamishinan ya yi kira ga ma’aikata a jihar da su kara yaba wa kokarin gwamnati ta yadda a kullum suke yin iya kokarinsu wajen jajircewa, “Amana da aiki tukuru don taimakawa gwamnati wajen cimma dukkanin kyawawan tsare-tsare da ta ke bi wajen daukaka ci gaban jihar baki daya zuwa wani matsayi mai girma”, in ji Kwamishinan.