Kaduna ta tura malamai 2,000 zuwa makarantu daban-daban

0
61

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tura malamai 2,000 zuwa makarantu 155 a fadin kananan hukumomi 23 da ke fadin jihar.

Gwamnatin ta yi haka ne a kokarinta na samar da ingantaccen ilimin yara mata a jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar, Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe ce ta bayyana haka a jawabinta ga wani bikin horaswa da Shirin Inganta Ilimin Yara Mata na AGILE da ya gudana a jihar.

An guadanaar da horasawan ne a karkashin ma’aikatar ilimi ta jihar, da kuma hadin gwiwar hukumar kula da malamai ta kasa reshen a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).

Shirin ya mayar da hankali ne wajen samar wa yara mata kara dama don cimma burinsu a rayuwa.