Zanga-zanga ta barke saboda rashin amincewa da sakamakon zabe – Brazil

0
53

‘Yan sanda a Brazil sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zangar da suka toshe manyan tituna a rana ta biyu bayan kayen da shugaban kasar Jair Bolsonaro, ya sha a babban zaben kasar da aka yi wanda har yanzu bai amince da sakamakon ba.

Sa’o’i 36 bayan sakamakon da ya nuna cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadi da maki 1.8 kacal, har yanzu Bolsonaro bai ce uffan ba, lamarin da ke kara nuna damuwarsa kan cewa yana iya kokarinsa ya kalubalanci sakamakon bayan shafe watanni yana kai hari kan tsarin zaben da aka ayyana a matsayin magudi.

A Novo Hamburgo, kusa da kudancin birnin Porto Alegre, ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa wata zanga-zangar, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Babban daraktan hukumar ‘yan sandan babban birnin kasar, Marco Antonio Territo de Barros, ya shaidawa taron manema labarai a babban birnin kasar Brasilia cewa, an samu toshewar tituna 267 a fadin kasar.

Masu zanga-zangar sanye da tutar Brazil, sun nuna rashin jin dadinsu da sakamakon zaben.

Tashin hankali na zuwa ne bayan yakin neman zabe mai cike da cece-kuce da aka yi Bolsonaro mai ra’ayin mazan jiya da kuma magajinsa Luiz Inacio Lula da Silva.